Ranar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ranar Hausa


Gabatarwa

Ranar Hausa, rana ce ɗaya tilo da aka ware a shekara domin gudanar da bukukuwan da za su raya al’adun Bahaushe a duniya. Dongane da yaushe wannan rana ta fara da kuma manufar yin hakan, abu ne da ya shigewa mutane da yawa duhu musamman waɗanda suke wajen ƙasar Hausa, amma dai akwai maganar cewa samar da wata keɓatacciyar rana guda ɗaya rak ya fara ne ta shafukan sada zumunta na Tiwita a ranar 26/8/2015.

Wannan rubutu zai yi bayani bakin gwargwado domin warware zare da abawa tare kuma da rabe barcin makaho da mai ido. Da fatan za a karanta wannan rubutu da buɗaɗɗiya kuma wankakkiyar zuciya mai shirin karɓar gaskiya.

Daga Tushe

Ranar 26 ga watan Agusta na shekarar 2015, ita ce ranar farko da aka fara yin rubuce-rubuce a kafar sada zumunta domin raya wannan rana. A ranar 26 ga watan Agusta na shekarar 2016, BBC Hausa sun wallafa cewa: “A ranar 26 ga watan Agusta ta shekarar 2015 ne dai aka fara bikin ranar ta Hausa a shafin na twitter”. Sanin takamaiman wanda ya fara yin wannan rubutu, shi ne abin da yake da wahalar tantancewa.

A wani bincike da na gudanar ta Intanet a ranar 24 da 25 ga watan Agustan 2021, na zaƙulo da dama daga cikin rubuce-rubucen da aka gudanar a wannan rana ta 26/8/2015 a wannan kafar sada zumunta ta Tiwita a lokacin da nake Accra, babban birnin Ƙasar Ghana domin halartar Bikin Ranar Hausa ta Duniya da aka gudanar a karo na biyu a ƙasar bisa gayyatar Cibiyar Nazarin Hausa da Al’adunta (Center for Hausa Research and Culture) da ke Ƙasar Ghana. Ga hotunan wasu da cikin shafukan da kuma abin da suka ce:


Koma dai yaya abin yake, an gudanar da taron ƙarawa juna sani game da al’adun Hausa a Wagadugu Babban Birnin Buskina Faso daga ranar 14 zuwa 15 ga watan Afirilun shekarar 2017; wato Exposition Hausa et Festival International de la Culture Hausa du Burkina Faso (FESTICHA). aTuranci Ingila kuma Hausa Exhibition and International Hausa Culture Festival of Burkina Faso wanda za mu iya kira da Taron Al’adun Hausawa Na Duniya a Hausance.

Ni Abubakar Muhammad Tsangarwa na samu halartar wannan taro tare kuma da gabatar da takarda mai taken Gudunmawar Shafukan Sada Zumunta Wajen Yaɗa Al’adun Hausa a Tsakanin Ɗaliban Kwalejojin Jahar Kano wadda za a iya ɗauka a nan.

Haka nan kuma dai na gabatar da wani jawabi a fadar Mai Martaba Sarkin Zango/Hausawan Lome da ke Ƙasar Togo, Alhaji Mamudu Ɗanbaba Keke III a ranar 22 ga watan Satumba na shekarar 2017 wanda a cikin jawabin nawa na nuna fai’dar ware wata rana da za a riƙa gudanar da bukukuwan da suka shafi raya al’adun Bahaushe a duniya kamar yadda za a iya gani da kuma sauraro daga wannan bidiyo da ke ƙasa:

A ta nawa ɓangaren, dukkan waɗannan abubuwa da na gatabar ban ci karo da waɗancan rubuce-rubuce da aka yi ta kar sada zumunta ta Tiwita ba; Allah bai kai hannuna kansu ba, kuma ban samu masaniya game da wannan ba sai a ranar 26/8/2018 na fara ganin irin waɗannan rubuce-rubuce da ke raya wannan rana a shafukan abokaina na Fesbuk.

Ƙari a kan haka kuma tun cikin shekarar 1994 nake da masaniyar gudanar da bukukuwa na tsawon mako guda da aka yi wa laƙabi da Makon Hausa a makarantun gaba da sikandire a lokacin da muke ɗalibta a Babbar Kwalejin Horas da Malaman Fasaha (Federal College of Education (Technical)) Bichi. Kuma har yau (2021), ana cigaba da gudanar da irin waɗannan bukukuwa na makon Hausa a wasu manyan makarantun Najeriya.

Manufa

A ta nawa ɓangaren, babban dalilin da ya saka na yi tunanin gabatar da wancan jawabi shi ne cewa a samar da wata rana guda ɗaya rak a duniya, tare kuma da sama mata gindin zama daga majalisar Ɗinkin Duniya, domin gudanar da bukukuwan da za su zama kafa ta raya al’adun Bahaushe don kar su ɓace kamar yadda na shaida a wasu ƙasashen Afirka da na ziyarta kafin wannan rana.

Kira

Ina kira ga al’ummar Hausawa ko’ina muke a faɗin duniya cewa mu yi ƙoƙari wannan rana ta zamar mana ranar farin ciki, annashuwa, haɗin kai, kyautata wa juna da kuma raya al’adun Hausa amma ba ranar huce haushi da cusa hausashi ba.

Ina fatan wannan rubutu ya zama sanadin ƙara haskaka fitilar inganta Ranar Hausa ta Duniya.

Manazarta

BBC Hausa (2016). Ana bikin ranar Hausa a Intanet. An ciro a 2021 daga shafin: https://www.bbc.com/hausa/labarai/2016/08/160826_world_hausa_day

Tsangarwa A.M. (2017). Gudunmawar Shafukan Sada Zumunta Wajen Yaɗa Al’adun Hausa a Tsakanin Ɗaliban Kwalejojin Jahar Kano. An ciro a 2021 daga: http://www.rumbunilimi.com.ng/TakarduGudunmawarShafuka.html

Abinci




Ɗakin Karatu

Harshen Turanci


Alƙur'ani


Jama'iyyun Siyasa

Kimiyyar Kwamfuta


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub